aba2397b e93b 468c 9b80 480fa9021e35

Kayan Aikin da Kake Buƙata Don Fara Coding

Bayan mun san menene programming kuma mun zaɓi harshen da muke son koya, tambaya ta gaba ita ce: Wadanne kayan aiki nake buƙata a kwamfuta ta don in fara coding?

Labari mai daɗi shi ne, ba ka buƙatar kashe kuɗi don siyan kayan aiki, dukkan abubuwan da kake buƙata kyauta suke. Ga manyan abubuwa guda uku da kake buƙata:

1. Kwamfuta (Kowace Iri Ce)

Kana buƙatar kwamfuta (Laptop ko Desktop) mai aiki da Windows, macOS, ko Linux. Ba lallai sai mai tsada sosai ba, muddin tana iya buɗe Intanet da rubutu, za ka iya koyon coding da ita.

2. Editan Rubutu (Text Editor)

Kamar yadda kake amfani da Microsoft Word don rubuta wasiƙa, haka ma kana buƙatar wata manhaja ta musamman don rubuta lambobin coding. Ana kiran waɗannan manhajoji da Code Editors.

  • Mafi shahara da sauƙin amfani kyauta ita ce VS Code (Visual Studio Code). Za ka iya sauke ta a kwamfutarka cikin sauƙi.

3. Manhajar Buɗe Yanar Gizo (Web Browser)

Kana buƙatar browser kamar Google Chrome, Firefox, ko Microsoft Edge. Idan ka rubuta kodin gidan yanar gizo a cikin VS Code, za ka buɗe shi ne a cikin Browser don ka ga yadda ya fito.

4. Intanet (Don Neman Ilimi)

Ko da yake za ka iya rubuta kusan dukkan coding ɗinka ba tare da intanet ba (offline), kana buƙatarsa lokaci zuwa lokaci don sauke manhajoji da kuma neman taimako a Google idan ka haɗu da matsala.

Yanzu kun shirya tsaf don fara tafiyarku ta koyon gina Websites da Apps!

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Save to list