1ecc0ec4 d5ef 471f 8aa8 825a59a09aa1

Harsunan Programming da Amfaninsu

Bayan mun fahimci menene programming a darasin farko, tambaya ta gaba ita ce: Wanne harshe (language) ya kamata in fara koya?

Kamar yadda mutane ke amfani da harsuna daban-daban a ƙasashe daban-daban, ita ma kwamfuta tana da harsuna daban-daban na programming. Ga manyan harsunan da suka fi shahara da amfaninsu:

1. HTML da CSS (Na Gina Websites)

Ko da yake ba a ɗaukar HTML da CSS a matsayin cikakkun harsunan programming, sune harsunan da ake amfani da su wajen gina kowane shafi na gidan yanar gizo da kuke gani a duniya.

  • Amfaninsu: Gina tsarin shafukan gidan yanar gizo (Websites).

2. Python (Mai Sauƙin Koyo)

Python shi ne harshen da ya fi kowane sauƙin koyo ga masu koyon coding a karon farko, domin rubutunsa yana kama da harshen Turanci na yau da kullum.

  • Amfaninsa: Nazarin bayanai, kera robots, basirar artificial intelligence (AI), da tsaron yanar gizo (Cybersecurity).

3. JavaScript (Na Sa Shafuka Su Yi Motsi)

JavaScript yana taimakawa wajen sanya gidan yanar gizo ya kasance mai motsi (interactive). Misali, idan ka danna wani maballi hoto ya fito, JavaScript ne ke yin hakan.

  • Amfaninsa: Samar da gidajen yanar gizo na zamani da wasannin kwamfuta.

4. Kotlin da Swift (Na Apps na Waya)

Idan burinka shi ne ka gina manhajojin wayoyin salula:

  • Kotlin: Ana amfani da shi wajen gina Apps na wayoyin Android.
  • Swift: Ana amfani da shi wajen gina Apps na wayoyin iPhone (iOS).

Wanne ya kamata ka fara koya?

Idan kai sabon koyo ne:

  • Idan kana son gina Websites, fara da HTML, CSS, sannan JavaScript.
  • Idan kana son gina Apps na Android, fara da Kotlin ko Java.
  • Idan kuma kana son koyon tsarin lissafi ko AI, fara da Python.

A darasi na gaba, za mu ga irin kayan aiki (software) da kake buƙata ka sanya a kwamfutarka don fara coding.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Save to list