About
Barka da zuwa HausaTech! Wannan dandamali ne na musamman da aka samar da shi domin yaɗa ilimin fasahar zamani, kwamfuta, da programming (coding) cikin harshen Hausa mai sauƙi da daɗin fahimta.
Burinmu (Our Vision)
A duniyar yau, ilimin fasaha da programming yana da matukar muhimmanci, amma yawancin darussan suna cikin harshen Turanci ne, wanda hakan ke yi wa matasa da ɗalibai da dama wahala.
A HausaTech, burinmu shi ne mu rushe wannan katanga ta yadda kowane mai jin harshen Hausa zai iya koyon yadda ake gina gidajen yanar gizo (Websites), kera manhajojin waya (Android Apps), da kuma sanin dabarun kwamfuta na zamani ba tare da wata wahala ba.
Abubuwan da Muke Bayarwa:
Darussan Kyauta (Free Lessons): Muna rubuta darussa daki-daki a kan harsunan programming daban-daban (kamar HTML, CSS, Python, da sauran su) domin koyo kyauta.
Littattafai (PDF Ebooks): Muna samar da ingantattun littattafai na musamman da za ku iya saya kuma ku sauke su a wayoyinku ko kwamfuta don zurfafa iliminku.
Manhajoji (Android Apps): Za ku iya samun gamsassun Apps da za su sauƙaƙa muku ayyukan kwamfuta da koyon programming.
Waye Ya Kafa HausaTech?
Wanda ya kafa kuma yake gudanar da wannan dandamali shi ne Malam Sulaiman Abubakar. Injiniyan kwamfuta ne mai sha’awar yaɗa ilimin kimiyya da fasaha ga al’ummar Hausawa, domin samar da matasa masu dogaro da kai a wannan karnin na fasaha.
Mun gode da ziyartar shafinmu, kuma muna fatan za ku amfana da dukkan darussan da muke gabatarwa!