Barkanku da sake haɗuwa a wannan sabon darasin!
Yanzu lokaci ya yi da za mu fara koyon ainihin harshen da ake amfani da shi wajen gina kowane shafi na gidan yanar gizo (website) a duniya, wato HTML.
Mene ne HTML?
HTML yana nufin HyperText Markup Language. Shi ba harshen programming ba ne na lissafi, a’a, harshe ne na tsara shafi (markup language).
Idan muna son gina gida, HTML shi ne bulo da siminti da katako na gidan. Yana gaya wa Browser abubuwan da za ta nuna a kan shafin gidan yanar gizo, kamar rubutu, hotuna, da bidiyo.
Ta yaya HTML yake aiki?
HTML yana amfani da abubuwa da ake kira Tags (alamomi). Kusan kowane tag yana da na buɗewa <tag> da kuma na rufewa </tag>.
Ga misalin kofin HTML mafi sauƙi:
<!DOCTYPE html>
<html>
<head>
<title>Shafina na Farko</title>
</head>
<body>
<h1>Barka da Zuwa Shafina!</h1>
<p>Wannan shi ne darasina na farko a koyon gina website.</p>
</body>
</html>
Ma’anar waɗannan alamomin (Tags):
- <html>: Wannan shi ne babban tag ɗin da ke nuna cewa dukkan rubutun na HTML ne.
- <head> da <title>: Wurin da ake sanya sunan shafin da zai fito a can saman browser.
- <body>: A nan ne ake rubuta dukkan abubuwan da muke son mutane su gani a kan shafin website ɗinmu.
- <h1>: Ana amfani da shi wajen rubuta babban take (Heading).
- <p>: Ana amfani da shi wajen rubuta dogon bayani ko sakin layi (Paragraph).
A darasi na gaba, za mu ga yadda za mu saka waɗannan lambobin (codes) a cikin kwamfutar mu ta VS Code kuma mu buɗe su a Browser don mu ga yadda suka fito!
